Sabbin labarai

Doko Android app dinmu ⬇ Download here

Buhari yace Sai Na Zarce Zaku San Abin Da Ake Kira Aiki



Sai na zarce zaku san abin da ake kira aiki – Shugaba Buhari
Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari yayi alkawarin cewa yan Najeriya zasu ga bambanci Idan suka sake zabar shi a zabe mai zuwa.
A 2015, Buhari ya jawo hankalin yan Najeriya ne da alkawarin habaka lalastaccen tattalin arzikin kasar, kawo karshen rashawa da cin nasarar yaki da Boko Haram.
Shugaban ya hori yan Najeriya dasu sake bashi dama ta biyu domin ya cigaba da aiyukan da ya fara.
Buhari Ya fadi hakan ne a jawabin da yayi wa yan Najeriya mazauna Amurka a ranar juma’a.
Buhari ya kara da cewa, babbar matsalar Najeriya itace manyan kasar da ke kwashe kudin kasar don azurta kansu.


Ya kuma tuna yadda ya garkame su lokacin da yayi shugabancin kasar a mulkin soja.
“A 1983, sojojin kasar suka nadani shugaban kasar. Na kwashe yan siyasar duk na zuba su a kurkuku, na sanar dasu gaskiyarsu kadai zata fitar dasu,”inji Buhari.
“Muka kwace abubuwan da suka sata, amma bayan nima an kulle ni, sai aka maidawa yan siyasar abubuwan da suka sata.
Wadanne masu kudin ne sukayi korafi akan haka?”
Shugaban kasar ya tuna lokacin da yake Chiyaman din PTF, yayi tituna daga Legas zuwa Abuja, zuwa Onitsha, zuwa Port Harcourt.
Tun daga nan ba a kara yin su ba, “Amma masu kudin basu ce komai ba akai,”
“Ana kira na baba-tafiya-a-hankali, amma wadanda ke gudun ina suka kai? “


DuniyarHausa



Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta DuniyarHausa .com  a wayarku ta hannu: 

Download here


Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:


No comments:

Post a Comment