Author Aisha Jega
Download here
Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito mun samu cewa, rai guda ya salwantar tare da jikkatar wasu Mutane uku yayin wata arangama da ta auku tsakanin rundunar sojin kasa ta Najeriya da kuma kungiyar ta 'Yan Shi'a cikin Garin Potiskum a jihar Yobe.
Rahotanni sun bayyana cewa, arangamar da ta auku a ranar Juma'ar da ta gabata ta kunno kai ne yayin da kungiyar ke yunkurin kawo karshen Muzaharar Ashura da ta gudanar da wasu Salloli da misalin karfe 8. 30 n safiyar yau daura da babban Otel dake garin Potiskum.
Kwamishinan 'yan sanda na jihar, Amdulmalik Sunmonu, ya bayar da tabbacin aukuwar wannan mummunan lamari yayin ganawarsa da manema labarai inda ya bayyana cewa, rikicin ya salwantar da rayuwar wani Mutum guda da kuma jikkatar wasu Mutane uku.
Yake cewa, kungiyar rundunar sa kai ta JTF ta yi gaggawar kwantar da tarzomar yayin da wasu mambobin kungiyar ta 'Yan Shi'a suka yi yunkurin raba wani jami'in tsaro da Bindigarsa na aiki.
Sai dai a yayin ganawar wani dan kungiyar ta Shi'a da manema labarai, Ibrahim El Tafseer ya bayyana cewa, ba tare da aune ba rundunar soji ta budewa mambobin su wuta da harasashai na Bindiga bayan sun kammala Muzaharar su ta Ashura.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta DuniyarHausa .com a wayarku ta hannu: Download here
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:


No comments:
Post a Comment