Sabbin labarai

Doko Android app dinmu ⬇ Download here

yadda Jonathan ya hau mulki bayan rasuwar ‘Yaradua Tambuwal ya bada labarin

Author Aisha Jega


Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana wannan ne lokacin da ya ziyarci Gwamnan Jihar Bayelsa Seriake Dickson domin yi masa ta'aziyya na rashin Mahaifiyar sa da yayi. A nan ne Gwamnan ya bada labarin abin da ya faru a baya.
Gwamnan na Jihar Sokoto yace irin su Seriake Dickson su ka same sa lokacin yana cikin manyan Majalisa inda su ka nemi a tabbatar da Jonathan ya gaji Marigayi Ummaru Yaradua domin ganin cewa kasar Najeriya ta zauna lafiya.

Hakan dai kuma aka yi Jonathan ya hau mulki bayan Yaradua ya bar Duniya. Tambuwal yace su ne su ka shirya yadda aka yi Jonathan ya tabbata a matsayin Shugaban kasa a tsakiyar 2010. Tambuwal yace ba tun yau ya san Dickson ba.
Wannan abubuwan sun faru ne tun lokacin shi Gwanna Seriake Dickson yana Kwamishinan shari'a a Bayelsa. Dickson ya godewa Tambuwal da ta'aziyyar da yayi masa inda yace irin su Tambuwal sun dade su na aikin ganin Najeriya ta zauna lafiya.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:


No comments:

Post a Comment