Author Aisha Jega
Duk wani abu mai rai daga karami yake farawa, sannan ya girma a hankali har ya zama gangaram! Soyayya ma ruhi gare ta, kamar shuka ce da ake dasawa a zukata, don haka tana bukatar raino da ban ruwa, kamar dai yadda ake yi wa tsiron da aka dasa. Idan haka ne kuwa, to ga wasu shawarwari na yadda ake rainon jaririyar soyayya, kamar yadda Abdullahi zaria (ays) ya bijiro mana da su:
.
1. A lura cewa akwai bambanci tsakanin rainon jaririyar soyayya da rainon soyayya. Zan yi bayani gaba kadan. Ta yaya za ka yi rainon jaririyar soyayya? Idan ya kasance akwai alkawarin wata a kanka kuma kana da bukatar hada zumunci na auratayya da su ko da ita ba tare da ka yi la’akari da kyau ko sura na yarinya ba.
.
Ma’ana, ka aminta da duk irin halin da za ka gan ta zuwa girmanta. To ya kamata a ce ka bi wasu matakai don samar da wanzuwar kauna da soyayya a tsakaninku na har abada ko kuma aure. Dole ne ka tabbata cewa tana sonka, idan ta soma mallakar hankalin kanta. Kuma kai ne za ka sanya mata sonka da kaunarka tun tana yarinya.
.
Ka guji yawan zuwa gurinta saboda zargi ko kazafi. Ka rika share hawayenta, ba ina nufin hawayen kuka na idanuwa ba. Ma’ana, ka rika saya mata abin da ka ga yaro yake so ko kuma burge shi. Mun san cewa soyayya ba ta da tabbas, to amma yin haka shi zai sa ba za ka cire rai ga barin sauyawarta ba, idan ta mallaki hankalin kanta. Kuma daga nan ma ka ga sai ka dasa da wani sabon yanayi na dauwamar da soyayyarka a kanta. Dole ne ka guji ba ta kyauta ko kudi ba tare da sanin iyayenta ba.
.
Dole ne ka rika nuna mata kauna da kulawa a koyaushe. Dole ne ka nuna mata muhimmancin rike alkawari saboda zamantakewarku ta dada karko. Dole ne ka yi taka-tsan-tsan da irin lafazi, kalamai ko hirar da kuke yi, musamman idan yarintarta ta yi yawa saboda kada ta je ta rika kwashe magana da surutu tana fada a ko’ina. Dole ne tsarin hirarku ya canja a duk lokacin da hankali ya soma karuwa.
.
Dole ne ka jure irin maganar da za ta yabo maka. Ka zama mai hakuri, sai ka ci galabar zama da ita da samun kanta a koyaushe. Ka sani a dukkan lokacin da ka ga ta isa mace mai hankali, to kada ka rika nuna mata cewa an ba da kai ne gare ta ko kuma ka rika fada mata cewa tun tana karama kake sonta, tun lokacin ba ta iya magana ba, da dai sauransu.
.
Yin haka zai tarwatsa tare da ruguza ilahirin ginin soyayyar da ka soma tunda fari. Kuma za ka iya rasa ta har abada. Muddin ba akwai wasa ba ne a tsakaninku. Mafi shawara ma, kada a yi saboda wasu ba su san wasa ba, ba kuma su iya ta ba. A duk lokacin da ta gane tsantsar mene ne so, to ka yi taka-tsan- tsan saboda so tsuntsu ne. Idan ta kai ma munzalin girma, soyayyarku da ita za ta tashi daga kan raino, yanzu sabon lale za ka soma, kamar yanzu ka ganta kana so; har zuwa lokacin da Allah zai sa ka aure ta.
.
Sai dai alakarku da ita tun tana yarinya za ta taimaka ma ka samu kanta cikin sauki, muddin za ka bi irin wanan hanya to za ka yi dace da kauna.
.
*** Madalla da wadannan shawarwari, da fatan masu son rainon soyayya za su dauki hannnu. - ***
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta DuniyarHausa .com a wayarku ta hannu:
Download here

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

No comments:
Post a Comment