Author Aisha Jega
Tsohon Shugaban Majalisar Wakilai na kasan ya bayyana cewa Gwamnonin PDP akalla 8 da kuma masu zaben ‘Dan takara da-dama su na tare da shi. Bayan Gwamnan ya leka Kudancin Najeriya ya kuma shiga cikin Jihar Kebbi.
Wani na-kusa da Tambuwal ya fadawa Jaridar This Day cewa tsohon Shugaban Majalisar Matashi ne mai jini a jika kuma wanda ya san darajar manya sannan bai da nuna banbanci don haka su ke ganin zai yi mulkin kasar nan a 2019.
Gwamnan na Sokoto Aminu Tambuwal dai yayi alkawarin gyara kasar nan idan ya karbi mulki inda yake cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya raba kan kasar nan kuma yana nuna karfa-karfa kamar ana mulkin Soja a Gwamnatin sa.
A Jihar Kebbi da ‘Dan takarar ya leka ya nemi manyan PDP su mara masa baya ya tika Buhari da kasa a 2019. Tambuwal yace Buhari ya jefa Jama’a cikin matsanancin yunwa da mugun talauci don haka yake neman ceto al’umma.
Jiya kun ji tsohon Shugaban Majalisar Wakilan Tarayya Aminu Tambuwal ya bada labarin yadda Goodluck Jonathan ya dare kan mulkin Kasar nan bayan rasuwar Ummaru 'Yaradua.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:


No comments:
Post a Comment