Sabbin labarai

Doko Android app dinmu ⬇ Download here

Tarbiyyar yara a bisa mahangar shari’a (1) By DuniyarHausa.com

Author Aisha Jega

bu na gaba da ya shafi makarantun boko, musamman masu zaman kansu, a gaskiya sai mun yi lura domin mafi yawansu tarbiyya kawai suke batawa.

Don haka ina kira ga al’umma mu tashi tsaye, domin ba wanda zai zo ya kawo mana gyara sai fa in mu muka nema da kawunanmu.

Makarantu tabbas na da tasiri, domin na san cewa a duk mako ko karshen wata ana tara yara a yi musu bayani wanda ya shafi rayuwarsu da wajibci ko hakkokin da iyaye suke da shi a kansu, a wani bangaren kuwa ’yan mata a koya musu ilimin zaman aure da hakkokin miji da su kansu angunan. In walimar biki ta tashi, malamai za su yi ruwa-da-tsaki wajen ganin sun fadakar da su a kan kula da hakkokin matansu. Kun ga a nan, rashin samun ingantattun malamai ko shakka babu al’umma za ta tabarbare.

Gwamnati uwa ma ba da mama:

Wannan ginshiki shi ne na karshe, a nan gagarumar matsalar take saboda rashin saka hannun gwamnati a kan abin da ya shafi tarbiyya da gyara akidun mutane.

Wannan kuma ya faru ne saboda irin tsarin mulkin da ake bi a kasarmu. Duk inda gwamnatin Musulunci take, za ka ga akwai dokoki wadanda suka shafi saka sutura ta kamala da sanya hijabi, wanda yanzu har ta sa yaranmu matasa maza suna saka kayan arnar Yammacin duniya irin su matsatsen wando ka ji ana ambatar wane ya yi shiga ko aski irin na BALATONI ko WIZZY ko SIWAGA da sauransu.

Haka gwamnati na da hakki na kula da kafafen watsa labarai don kada su kuskura su saka wani shiri ko fim wanda ya saba wa addini ko al’ada.
Kai, in zan ci gaba zan cinye duk filin a kan nauyi da gwamnati take da shi wanda kuma shi ya jawo mana yanzu matasanmu ba su da kunya ba kuma tsoron Allah.

Allah Ya shiryar da mu baki daya.
Gudunmawar jama’ar gari wajen gyara ko akasin haka ga matasanmu:

Kamar yadda na yi muku alkawari yau cikin yardar Allah zan tsakuro kadan daga cikin irin gudunmawar da al’umma kanta ke bayarwa wurin saita kwakwalwar matasan mu. An ce in an bugi jaki to a bugi taiki.

Tabbas iyaye da malamai da sarakuna wani lokaci da gwamnati, in sun yi iya kokarinsu, sai ka samu in yaranmu suna cakuda da al’ummar da ta gurbata a karshe sai ka ga mai doki na neman komawa kuturi. Hausawa na cewa “zama da madaukin kanwa. shi yake kawo farin kai” Kuma Hausawa na cewa “An baro gini tun farko...” Inda tun farko iyaye sun dasa wa ’ya’yansu tsoron Allah to ina tabbatar muku da babu shaidanin da zai gamu da yaronka ya zo masa da wani abu sabo.

Amma duk da haka, zan yi kira ga al’umma baki daya mu tuna cewa muna da ’ya’yan nan. In ma ba ka da su to ai kana da kanne, ko yayye kai ko ba ka da ko daya, ai kai ma haihuwarka aka yi.
Saboda an ce “da” (yaro) na kowa ne, Kuma an ce ka so naka duniya ta ki shi, Kuma ka ki shi duniya ta so shi.

Kuma ina kira gare mu, mu sani, kula da tarbiyyar yara ba sai iyayensa kawai ba, mu koma baya mu ga yadda uban wani ke ladabtar da dan wani wanda yanzu ba haka abin yake ba.
Zan dakata a nan da fatar Allah Ya shiryi zuriyarmu baki daya.

Sanusi Hashim Abban Sultana, Katsina

No comments:

Post a Comment