Author Maryam Ahmad
Haihuwa kamar yadda kowa ya sani Allah ne ke ba dashi ga wadanda Ya hukunta zai basu haihuwa. A irinSa, shike bada haihuwa maza zalla ko kuma mata zalla ko ma Ya hadawa mutum duka biyu wato maza da mata banda Allah babu wanda yake wannan kyautar don haka shine abun dogaro ga wadanda basu samu haihuwa ba hakan kuma shi ne abun godiya ga wadanda Ya albarkacesu da haihuwa ko maza zalla ko mata zalla ko kuma wadanda Ya yiwa hadakar maza da mata.
Haihuwa 'ya'ya mata ba karamin baiwa bane da daraja ga wadanda Allah Ya albarkacesu da samun 'ya'ya mata ko da kuwa guda dayace, ko ma riko kuke yi na 'ya'yan 'yan uwa ko abunda yayi kama da hakan, to yana da matukar kyau ku dauka cewa tarbiyan wannan 'yar yana da matukar amfani a gareku.
Babu shakka tarbiyan yara ga iyaye ko magabatansu abun tambaya ne ranar gone kiyama ga wadanda Allah Ya daurawa hakkin yin haka. Sai dai kuma tasirin tarbiyan 'ya mace ya dara na 'ya'ya maza nesa ba kusa ba idan akayi la'akari da tasirin da 'ya mace take dashi wajen ci gavan al'uma ko kuma lalata al'uma.
A shekeru kamar 4o da suka gabata, a lokacin da ba a samu ci gaba da wayewa irin na zamani ba, tarbiyan 'ya mace yana da matukar sauki ga iyayenta ko masu rike da ita. Ganin a waccan lokacin kowa yana daukar dan wani shima dansa ne don haka zai iya hukuntashi babu wani tararrabi ko shakku cewa iyayensa zasu ji zafin duk wani matakin da aka dauka na ladabtarwa akan yaran wanda babu wannan tsarin a yanzu.
Haka kuma abubuwa na ci gaba masu gyara da bata tarbiya da ake dasu a yanzu babu su a shekarun baya.
A wannan mukalan ina sone na kawowa iyaye Irina yadda zasu yi tarbiyan 'ya'yansu mata dai-dai da zamani wanda haka zai iya taimakawa wajen samar da tarbiya mai inganci kuma a zamance ba tare da kaucewa tsari na al'ada ba bare kuma addini.
Mataki na farko ga wadanda aka haifa musu 'ya mace shi ne su tabbatar da cewa sun sanyawa jaririyar nan suna maiko mai asali da kuma tarihi. Babu shakka shi suna yana da matukar tasiri a rayuwar mutum. Akwai wasu sunayen da sai ka dauka mata kayawawa ne kadai ake basu wadannan sunaye da wuya kaga mace mara kyau da irin wannan sunan. Kamar yadda ake da sunaye na mata dolaye, duk yar da kajita da wannan sunan ko mai kyauta zaka samu tun tana karama doluwace. Haka nan mata ma fadata da masu hakuri a suna kawai kana iya ganesu duk kuwa da wannan camfin ba wai lalle bane ya zama hakan amma dai abun bukata ga iyaye shine suyi kokarin samarwa 'ya'yansu mata sunaye masu kyau.
A lokacin da 'ya mace ta soma tasawa abunda ya kamata iyaye zasu maida hankali a kai shine samar mata kayan wassannin da zasu bude mata kwakwaluwa, da kayan wasan da zasu daurata akan matantakanta. Bazai yiyu iyaye su saiwa 'yarsu ball ko dokin roba ba a matsayin kayan wasanta. Abubuwan wasannin irin su baby roba, kayan kwalliya, kayan kicin, da ireirensu sune abunda 'ya mace take bukata a matsayin kayan wasanninta.
Daga shekarun 3 zuwa 5 a wannan lokacin iyaye ya kamata su soma daura yarsu mace akan yadda ya kamata tayi kwanciyar barci, zama a cikin mutane, hanata rowa da kwadayi da tsawatar mata akan yawan surutu.
Ba kowani makaranta bane iyaye zasu tura 'yarsu mace ba. Yana da kyau ko nace ya zama dole a lokacin da zasu sanya 'yarsu makaranta na zamani ko ma na addini su tabbatar da ingancin wannan makarantar, da kuma tarihin shugabannin makarantar dama masu koyarwa a makarantar domin sanin makarantar ta dace da akidar da kakeson daura 'ya'yanka akai musumman kuma 'ya mace. Ka tabbatar da cewa malaman dake makarantar maza basu da tarihin cin zarafin 'ya'ya mata kanana.
Wannan binciken yana da matukar amfani domin su malamai sune na biyu a masu taimakawa iyayen inganta tarbiya ko lalatawa. Zai iya yiwuwa ku kuna kokarin yiwa 'yarku tarbiya mai kyau amma tana zuwa makaranta ana rusashi ganin wannan shekarun duk abunda aka cusawa yaro ya sauna kenan.
Abu na gama a lokacin da 'yarku ta soma tasowa shine kula da irin kawayen da take mu'amala dasu, 'yan unguwane, makotane ko kuma makaranta ko aji gudane ya hadasu, babu shakka wannan yanada amfani ga iyaye domin bai yiwuwa iyaye su bar 'yarsu tana mu'amala da wata kawar da basuda tarihinta ko na gidansu ba, wanda yin hakan kuskure ne sosai dole ne a taya ta tace mutanen da zatayi mu'amala dasu don gudun warware kokarin tarbi'yan da iyaye ke kokarin ginawa.
Ga iyayen da suke burin sun samarwa yarsu tarbiya na zamani mai inganci, abu na gaba mafi mahimmanci shine kula da kuma zaben al'umar da kake son rayuwa a cikin ta. Tabbas al'uma da ake cinta kuma ake cudanya da ita tanada matukar tasiri a irin tarbiyar da iyaye suke son ganin sun tarbiyantar da iyaye su cikinta musamman ma ya mace.
Bazai yiwu ba kanason yiwa 'yarka tarbiya mai kyau amma kuma ka zauna cikin al'umar da zina ko shan giya ba matsalarsu bane. Ko masu ganin sata ma sana'a ce. Don haka dole ne iyaye su tantance cikin al'umar da zasu zauna cikin ta domin taimaka musu wajen ginawa 'ya'yansu musamman mata tarbiya mai nagarta.
I lokacin da 'ya mace ke tasowa, a lokacin ne ya kamata iyaye maza su jawosu a a jiki sosai domin cusa musu wasu akidu ko ra'ayoyin da kake bukatan daura yarka akansu. Irin tsoratar da ita akan kin Allah ko rashin bauta maSa da kwadaita mata abubuwa najin dadi idan aka bi Allah da maganar iyaye. A irin wannan lokacin idan burinka tayi karatu ne zaka alkawarta mata wani abu dakasan tafi so da sha'awa idan har tana kokari a karatu.
Mataki mai hadari wanda kuma shine yake bukatar hikima, sa ido da kuma addu'ar iyayen wajen tarbiyar 'ya mace a wannan zamanin shine a matakin da ta balaga.
Idan Allah Ya bani iko zamu ci gaba a rubutuna na gaba. Amma kamin yana da kyau iyaye su fahimta tarbiya yara yana tafiya ne tare da musu addu'a na alheri da fatan neman musu shiryiwa wajen Allah ba tunanin dabarun bane kadai zai daura yaranmu kan tarbiya nagari ba.
Allah Ya sa mudace, Ya bamu yara masu albarka Ya kuma shirya manasu kan hanyarsa madaidaiciya.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta DuniyarHausa .com a wayarku ta hannu:
Download here

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

No comments:
Post a Comment