Sabbin labarai

Doko Android app dinmu ⬇ Download here

Sojoji Da Boko haram: Anyi musayar wuta tsakanin yan Boko Haram da Soji a Damasak

Author Aisha Jega 

Jami'an sojin sun shiga musayar wutan ne yayinda ya Boko Haram suka kawo musu hari a inda suke zaune misalin karfe 6 na yamma. Tun lokacin ana ruwa harsasai.
An samu wannan rahoto ne daga kakakin hukumar sojin Najeriya, Birgediya Janar Texas Chukwu.
Daga baya, hukumar sojin Najeriya ta bayyana cewa an samu nasarar kashe dimbin yan Boko Haram a wannan artabu da ya faru a Damasak. Kana ta kara da cewa yaki da yan ta'adda na cigaba da samun nasara a yankin Arewa maso gabashin Najeriya.
Hukumar ta karyata rahoton Sahara Reporters cewa yan Boko Haram sun fitittiki Sojoji kuma sun kwace garin Damasak. Ta yi kira ga kafafen yada labarai da su guji yada jita-jitan karya ga al'umman Najeriya.
A karshe, hukumar ta shawarci mazauna yankin da su fita harkokinsu na ya da kullum saboda hukumar na tabbatar musu da cewa za ta kare rayukansu da dukiyoyinsu.
Kwanakin bayan nan yan kungiyar tada kayar bayan Boko Haram sun dau sbaon salon kaiwa jami'an soji hari a barikinsu sabanin kunar bakin wake da suke tura yara. Wannan ya haddasa hallakan rayukan sojoji da dama musamman a Gudumbali

No comments:

Post a Comment