Sabbin labarai

Doko Android app dinmu ⬇ Download here

Shugaba Buhari ya caccaki majalisar dokoki bayan an kwato N769bn na kudaden sata

Author Aisha Jega
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a jiya Talata, 11 ga watan Satumba ya caccaki majalisar dokokin kasar akan jinkiri wajen gabatar da dokar hukunta masu laifi da aka gabatar mata.
Buhari wanda yayi magana a lokacin da kwamitin da shugaban kasa ya kafa don tantance kudaden da aka kwato suka gabatar da rahotonsu, yace makamin da zai inganta kudaden da aka kwato shine gabatar da dokar.

Ya kuma bukaci majalisar dokokin kasar da su dauki matakan da suka dace wajen gabatar da dokar.

Ya ba yan Najeriya tabbacin cewa gwamnatinsa zata ci gaba da jajircewa kan alkawarin da ta dauka na yakar cin hanci da rashawa da kuma kalubalen tsaro.
Ya bayyana cewa za’a yi nasari cikin tsanaki akan bincike da shawarwarin kwamitin domin yin aiki da su.

Shugaban kasar yace cin hanci da rashawa ya kasance barazana ga ci gaban kasa, tsaron kasa da kuma tattalin arzikin Najeriya.
Buhari yace ya zama dole a dauki matakan yin amfani da kamun wajen magance matsalolin tattalin arziki da na jama’a, sannan kuma ya zama dole a toshe duk wata kafa ta satar kudaden jama’a.
Kwamitin mutane uk sunce sun samo zunzurutun kudi har naira biliyan 769 a lokacin da tayi tana bincike.

No comments:

Post a Comment