Author Fatima
Wasu mutane da ake zargin makiyaya ne sun yi awon gaba da mata a wani hari da suka kai kauyukan Gwon, Bolki da Nzumosu a karamar hukumar Numan da ke jihar Adamawa.
Garuruwan da ke cikin karamar hukumar Numan na ci gaba da fuskantar hare hare tun daga farkon watan Janairun wannan shekarar, hare haren da hukumomi ke kallon ya zarce a kirashi da rikicin makiyaya da manoma.
Da ta ke tabbatar da faruwar harin, yar majalisa mai wakiltar mazabar Numan a majalisar dokoki ta jihar, Mrs. Sodom Tayedi ta shaidawa manema labarai cewa makiyayan na ci gaba da mamaye sauran garuruwan da ke makwaftaka da su.
Ta bayyana cewa zuwa yanzu ba'a san adadin mutanen da lamarin ya shafa ba, sakamakon mutane sun gudu don buya a cikin dazuzzuka.
Hon. Tayedi, ta yi ikirarin cewa maharan sun fito ne daga yankin Abbare, inda ke da tarin sojoji a wajen.
"Akwai sojoji a Abbare, amma hakan bai hana maharan fitowa daga yankin ba" a cewar ta.
Ta ci gaba da cewa: "Babu wani lokaci da suka kawo hari, ni kuma ban kira jami'an tsaro ba a matsayina na wakiliyarsu. Yanzun nan na kira kwamandan wata runduna, ya tabbatar min dakarun soji na zuwa yanzu"

No comments:
Post a Comment