Sabbin labarai

Doko Android app dinmu ⬇ Download here

Ruwan-Ido Ke Janyo Wa Wasu ‘Yan Matan Rashin Samun SOYAYYA

Author Aisha Jega 
Babban abin da yake dada janyo wa wasu ‘yan matan rashin samun mazajen aure shi ne ruwan-ido.

Da yawan ‘yan mata yayin da suka kai wani mataki na girma tauraruwar su na haska wa a wannan lokacin wanda hakan ke sa wa samari su rinka tururruwar zuwa wajen yarinya don zama masoyanta na aure da wanda ba na aure ba.
A wannan mataki ne ita budurwar take ganin ta zama tauraruwa wanda hakan yakan sa ta ruwan-ido wajen zabar masoyi na kwarai kuma na gaskiya wanda yake sonta tsakani da Allah.
‘Yan matan sukan zabi masoyi yayin da suka sami wanda ya fi shi sukan canja akalarsu kan wanda idanuwan su ya gano, haka za su yi ta canja wa har su rasa wanda za su zaba.
Kyale-kyale da rudin duniya yakan saka idanuwansu rufewa su rasa gane ina suka dosa.
Ba wani abu ba ne yake janyo hakan illah kwadayi da kuma son abin duniya shi yake kawo hakan wani sa’in ma da karance-karancen littafin Hausa da yake tasiri cikin zuciyarsu.
Da yawa a yanzu sukan dauki buri mai girma su dora wa kansu wanda hakan ko kusa ba zai samu ba idan kuwa ya samu to! Sai an sha wuya ko kuma a same shi da sauki karshe a sha wahala.
Wasu sukan saka wa zuciyarsu cewa lallai sai kyakkyawan saurayi zukeke mai hanci dogo shi ma dogo fari kamar zubin Fulani irin saurayin cikin littafin Hausa.
Sai mace ta sakawa zuciyarta ita a lallai sai irin wannan namijin za ta aura wanda yake mara makusa kamar shi ya yi kansa, ko kusa babu wannan ba zance babu kwata-kwata ba amma kafin a samu za a dade a ce an samu wanda ya hada komai ba shi da wata makusa kamar yadda na cikin littafin Hausa yake.
Wasu sukan saka wannan a ransu duk saurayin da ya zo sai su ce ba sa so saboda sun ruga sun bar wa zuciyarsu wannan tsarin.
Ko kuma mace ta kudurce cewa lallai sai mai kudi saboda mijin kawarta ko saurayin kawarta mai kudi ne, don haka ita ma sai mai kudi ko kuma ajinta ya wuce ta auri talaka ko wanda sana arsa ba mai girma ba ce irin wadda duniya za ta san da zamansa ba.
Iri-irin wadannan dama wasu ra’ayoyin nasu wandanda ban fado su ba, toh! Yakan saka wasu matan rowan-ido don ba duk-kane aka taru aka zama daya ba, sai an amincewa saurayi ringidi-ringidi da zarar wanda ya fi shi ya zo sai zance ya sha bamban.
Mata sai kun mun hakuri domin yau shafin nawa naku ne, ki sani cewa yayin da kika tsaya rowan-ido za a kai ki a baro ki ne komai kyanki.
Mata sukan rasa na zaba har lokacin da samarin za su daina zuwa lokacin mace ta huce wannan matakin da tauraruwar tata take haskawa sai kuma ta dawo tana lissafa adadin samarin da ta yi tana da ta sani tun a wancen lokacin ta zaba da ya fi mata yanzu ga shi tana zaune ana aurar da kannenta tana gani.
A cikin rowan-idon wasu sukan kudurce su ba za su auri mai mata ba wani lokaci ma har iyaye sukan ba wa yaranau gudun mawa wajen haifar da ruwan idon yayin da akaita zaben aka rasa sai a dawo ana addu’ar Allah ya kawo koda mai mata uku ne saboda burinsu a lokacin a aurar kar masu zaman unguwa su rinka ci gaba da zagi ko kuma saka ido a kowanne motsi na yarinyar.
A cewar wasu ‘yan matan zama da sautayi daya tsautsayi ne, gwara su rana kafa har Allah ya sa a dace, sai dai kuma abin takaicin shi ne za ku ga wasu mazan na arziki wa ‘yanda suke da niyyar yin aure kuma sun je wajen yarinya da zuciya daya amma ita sai ta ki amince wa da soyayyarsa koda kuwa ba shida wani makusa a tare da shi safi biyewa samari matasa wadanda ba su da niyyar yin aure a wannan lokacin wato maza ‘yan tayin hira su rudeta su janye zuciyarta da wasu abubuwan wanda ita a lolacin ba za ta san hakan ba sai ranar da ta yi hankali ko lolacin da ta saninta ya zo.
Ina kira ga masoya musamman mata tunda batuna gareku nake a yau da ku daina rowan-ido su tsaya su kula wajen zabar miji na-gari, don gudun da na sani wata rana wasu mazan sukan zo wa ‘yan mata da abubuwa daban-daban don janye zuciyarta wanda a bayan auren mace za ta ga ba hakan yake ba sai kuma ta yi da ta sani wane ta zaba sai a lokacin za ta rinka hango halayyar wancen wanda ta bari ta yi da ta sani ta dauke shi, da na sani dai keya ce.
Wata ma garin rowan-idon ta zabo wa kanta wanda kullum zai rinka jibgarta ko kuma wanda zai rinka hanata abinci, don akwai masu kudin da ba sa iya fitarwa cikin gidansu ba sa ba wa iyalansu komai sai dai a rinka gyara ginin gida ko shi ya dinga dinki yana canjawa ana alhaj wane mai kudi ne amma fa cikin gidan sa iyalai na kuka ‘yan mata sai a kiyaye.
Haka zalika akwai namijin da za ki dabe shi don gayunsa amma bayan an yi aure sai lamari ya canja wannan dan tsukewar da yake yi yana janyo zuciyarki sai ki ga duk ba hakan yake ba sai zai futa yake samun daman yin wanka ma in har zabai futa ba toh ba shi ba wanka kinga ba labari lamari ya baci sai a kula don gudun da an sani an zabi mai shigar kammala wanda yake sako ta-zarce ana kushe shi ana cewa bai waye ba.
Ruwan-ido yakan korarwa da mace samari karshe ta zo tana da ta sani. Masoya sai a kula a rinka danne zuciya a nutsu a yi aiki da hankali wajen zabar mijin aure don kar a yi zaben tumun dare.
Sanfuran Kalaman Soyayya
Muna son junanmu kuma yanzu mun gama zama daya amma mai ye laifina don na mamaye zuciyar kyakykyawa kamarki?
Ina ma a ce kikalli mudubi ki ga tsabar kyan halittarki dole na riritaki na kula da ke domin ba zan yi wasa ki kubuce min ba.
Ni na san wahalar da na sha har na same ki tabbas ke mai daraja ce kuma ba zan mi ki kishiya ba.
A hankali ga shi zuciyata ta kamu da cutar da ke kadaice mai maganinta babu maganar na guje to ina ma zan je na samu nutsuwa sama da gunki masoyiyata
Ke ce idona yake son kallo a kodayaushe kallon hotonki ya zamar min aiki wallahi ke kyakykyawa ce wannan zumar ta soyayya zan ci gaba da lasa miki muddin za ki sha daga koramata.Ke hasken rana ce da ke dusashe dukkan duhu, da daddare kuwa ke ce farin wata sha kallo, kuma ke ce tauraruwar da take haska sararin samaniyar zuciyata
Kyallin kyawun fatarki kadai kan haddasar da hargitsin nishadi a zuciya sanda na tuno da hakan
Dukkan hakkin soyayya zan ba ki tunda kin ban ragamarki a hannuna da kuma sanyaya ranki ke ce zara ni wata. Zan so a ce kina gefena dakin juya ni za ki gani a damarki ni na riga na mallaka kaina gareki komene zan miki ba na kokonto tunda na gane ke ce mai sona.
Kin san walwalarki ita ce sinadarina na warwasawa.
Ka gode Allah domin kuwa kana da babbar baiwa ta kalamai wadda duk wata ‘ya macen da ta ji su dole su shiga cikin jikinta har ya sata walwala koda kuwa ranta a bace yake lokacin ina alfahari da kai zamowa gwarzo gareni kuma jajirtacce wajen bayyanar da ingantacciyar soyayya gareni mai dauke da nishadi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta DuniyarHausa .com  a wayarku ta hannu: 

Download here


Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:


No comments:

Post a Comment