Sabbin labarai

Doko Android app dinmu ⬇ Download here

QALUBALE GAREKU MATA MASU ZAFIN KISHI By DuniyarHausa.com

Author Fatima

Dukkan yabo da gtabbata ga Annabin mu Muhammad sallallahu alaihi wasallam.

Nazabi yin wannan lacca sabida ganin yanda idanun mata suka rufe sabida zafin kushi komai suna iya aikatawa Haqiqa kishi abune mai kyau ga ma'aurata mace ko namiji ko Wanne yaji yana kishin Dan uwanshi ammafa ta halattaciyar hanya ba irin hanyoyin da mukebi yanzu ba muna quntatawa juna wai kuma dasunan so wane irin so ne wannan?

_Kishi Kala biyu ne akwai:_

_a Na halak_
_b Na haram_

      _Kishi na halak shine: dole munsan duk Matar da take matuqar qaunar mijinta sai yakasance tana kishi a kansa amma zatabi duk Wasu hanyoyi ne da Allah ya yarda dasu wurin wanzarda kishinta gareshi. Misali:_

     _Waccen matar tana yimai wani abin dayafi kulata kaina to ya zanyi yadawo hannuna? Sai nima in nemi Wata hanya ta kyautatawa inriqa yimai namiji kamar qaramin yaro ne yanda kikasan kina juya yaro wanda baisan komai ba  haka zakijuya dattijo dan shikara hamsin wlh indai ya sami kulawa ta musamman to ina tabbatar miki ba abinda zaku ce kina nema baki samu ba._

_kishi na haram kuma shine: to idan muka duba yanzu dayawan mu haramtaccen kishi muke misali:_

     _wata sabida Tsabar kishi takanbi duk Wasu hanyoyi Dan taga tahana mijinta qara aure koma idan yayi za'ayi qoqari tabi Wasu hanyoyi ta rabasu Haba yar uwa!_

    _way da Allah zakuyi jayayya ne ko da Manzon Allah?  Allah fa cewa Yayi:_

      _(maza) KU AURI ABINDA YA MUKU DADI DAGA MATAYE BIBBIYU KO UKU UKU KO HURHUDU Sa'annan yace IDAN KUNJI TSORON BAZAKU IYA ADILCI BA TO KUTSAYA AKAN DAYA. aa to Yaruwa kaduba fa dayarce ta qarshe Shima idan bazai iya yin adalci bane zai tsaya kanki ke kadai to Ashe bamuso mazajen mu su kasance masu ADILCI._?

_Zai yu Wata tace kishi kuma? Eh kishi yar uwa._

     _Zafin kishi Wata hanyace da take wargaza aure kuma take hada mai yinshi da nadama da dana sani maras amfani._

_Zafin kishi yana haddasa fitintinu masu tarin yawa gaduk matarda ta tsawwalawa rayuwata da shi zuku ganta kullum cikin rashin kanciyar hankali take_

_Zaiyu wata tace wai kishin nan ba har matan Annabawa da sauran bayi na gari sunayi ba?_

_Eh Tabbas matan Annabawa da sahabbai suma suna da kishi amma ba irin naki ba yar uwa_
      _Su sunyi kishi ne yanda Allah ya umarta  sunyi kishi Dan mijinsu ya amfana dasu dan kawai neman yardar miji da neman yardar Allah a lahira kowacce tana neman tasamu soyayya da qauna a wurin mijinta_
_shiyasa Daga cikinsu Wata zata iya sadaukarda kwananta ma Wata sabida ba shine damuwar ta ba aljannah ce kawai burinta ba duniya ba_

*JAN HANKALI*

YAKE YAR UWATA KI GUJI YAWAN BINCIKE YAWAN ZARGI WA MIJIN KI BINCIKE DA ZARGI WALLAHI SUNA SAURIN WARGAZA AURE KO MANZON ALLAH YAYI MUNA HANI DA BINCIKE

AWANI HADITHI YAKE CEWA:
*YANA DAGA KYAWUN MUSULUNCI MUTUM YABAR ABINDA BAI SHAFESHI BA*

MIJI YA AJIYE WAYAR SHI KIN DAUKA KINA TSANANTA BINCIKE AKAI MIYA SHAFEKI DA DUBA WAYAR SHI?  ZAKI JE GARIN BINCIKE BIKCIKEN KI KI TONO ABINDA ZAIYI SANADIN AUREN KI KOMA YAYI SANADIN RAYUWAR KI BAKI DAYA KINGA KIN JEFA KANKI CIKIN MATSALOLIN RAYUWA.

KO KIGA MIJI YA AJIYE EN TAKARDUNSA KIZO KINA BINCIKAWA TO KIKA SANI KO WATA CEN TADAN AIKOMAI DA WASIQAR SOYAYYA KINGA KIN TONOWA KANKI ABINDA ZAI HANAKI BACCI

Wai shin ba'a aure ke aka auro ki amma sabida tsabar jahinci kiyi kane kane a gida ga mata birjik a gari sunata fadawa halaka sabida rashin aure amma kinqi ki bari a tsamo raywarsu daka duhu zuwa haske shin hala bakida qanne, yaya, yanuwa mata ne? Su idan sun tashi aure duk samari zasu aura ne?

[11/21, 8:45 PM] أم أبوبكر الصديق: _Ina yimiki kashedi da kishi! Domin shi kishi mabudin saki ne, kuma Ina yi miki kashedi da yawan zargi domin yawan zargi yana kawowa qiyayya._
[11/21, 8:45 PM] أم أبوبكر الصديق: _Allah ya sa mugane cewa tsakanin kishi bashine hanyar janyo soyayyar mazajen mu agaremu ba kyautatawa da mutun tawa da bada kulawa ta musamman yagano cewa Zaki iya sadaukarda komai akansa shine zaisa kisami so da qauna a wurin Mijinki yaji bazai iya rabuwa dake ba koda na kwana daya ne.

_shi mummunan kishi yana wargaza gida ne gaba daya shiyasa mata nagari sukan nisance shi domin Yakan gusarda kwarjini, darajar Ki, qimarki,  soyayyarki acikin zuciyar mijinki batare da kinsan dalili ba Yaruwa_.

_YAKE YAR UWATA KI SANI QARIN AURE NI'IMA CE QARIN AURE IBADA NE QARIN AURE SUNNA NE  MANZON ALLAH SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM YACE AURE SUNNAH TA CE DUK WANDA YA KYAMACI SUNNA TA TO BAYA TARE DANI ALLAH YASA MUYI RIQO DA SUNNAR ANNABI MUHAMMAD SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM Allah ya ganar damu Gaskiya yabamu ikon bi ya nunamuna qarya yabamu ikon guje mata._

       *DAWANNAN NAKE CEWA SADUWAN ALKHAIRI SAI WANI LOKACI IDAN ALLAH YA AMINCE*

```أختيكم في الإسلام``` 
```أم أبوبكر الصديق```

       ```سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله الا انت استغفرك وأتوب إليك ```

السلام عليكم ورحمة الله وبركا ته.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta DuniyarHausa .com  a wayarku ta hannu: 

Download here


Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:


No comments:

Post a Comment