Sabbin labarai

Doko Android app dinmu ⬇ Download here

Photon Wani matashi da aka cafke yayin da yake lalata allon takarar Buhari

Author Aisha Jega 
Mun samu daga National Helm cewa jam'ian 'yan sanda da ke babban birnin tarayya Abuja sun kama wani matashi da aka samu da rana tsaka yana lalata allon takarar shugaba Muhammadu Buhari.
An gano matakin ya yanke shawarar lalata allon takarar ne saboda wai bai gamsu da yadda harkoki ke tafiya a kasar ba sai dai hakan bai hana 'yan sanda tisa keyarsa ba

A watan Augusta da ta gabata, hukumar 'yan sandan jihar Kano sunyi gargadi cewa duk wani da aka samu yana lalata fostan takarar shugaba Muhammadu Buhari zai fuskanci fushin hukuma.
Yan sandan sun bayar da wannan sanarwan ne bayan an samu wasu matasa na lalata fostoci ta hanyar yage su ko kuma kwakwule sassan hoton da ake kyautata zaton 'yan jam'iyyun adawa ne ke aikata hakan.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Magaji Majia ya ce hukumar ba baza jami'anta masu saka unifom da masu saka kayan farar hula domin sa ido kan wadanda ke lalata fostoci a sassan jihar ta Kano.
A cewar Majia, ya zama dole a dauki tsatsauran mataki bayan wasu bata gari da ba'a san ko su wanene ba sun lalata allon takarar shugaba Buhari da ke kan titin Sharada a Kano.

No comments:

Post a Comment