Author Fatima
Nasiha yaye masu neman raba auren ’ya’yansu
Masu bibiyar wannan shafi ina yi muku sallama irin ta addinin Musulunci, Assalamu Alaikum. Barkanmu da sake haduwa a wannan fili mai tarin albarka inda muke tattauna batutuwa don fadakar da juna ko yi wa juna nasiha a kan abubuwan da suka shafe mu.
To kamar kowane lokaci, yau zan tabo wani batu ne da yake ci mana tuwo a kwarya. Wannan batu shi ne na yadda wadansu iyaye suke yunkurin raba auren ’ya’yansu ba tare da wani dalili ba.
A wani lokaci irin wadannan iyaye za ka tarar ba su da wata hujja amma saboda son rai ne suke haka. Ina amfanin uba ko uwa su aurar da da ko ’ya amma su rika neman raba auren. Wace irin riba za su samu idan suka yi haka?
Irin wannan matsala takan shafi bangaren mace da na namiji, sai dai abin ya fi kamari ne a bangaren mace.
A wasu lokuta kuma za ka tarar abin yana faruwa ne idan iyaye maza suka nuna lallai sai dansu ya rabu da matarsa watakila saboda ba sa ga maciji da ita. A kan haka sai ka tarar dan ya shiga matsala domin yana son matarsa hasali ma suna zaman lafiya amma tun da iyayensa sun nuna lallai sai ya rabu da ita sai ka tarar ya fada cikin matsala. Idan aka yi sake har ya rabu da matar da yake kauna, to da wuya ya sake yin wani sabon auren cikin sauki. A wasu lokuta irin wadannan maza kan bar garuruwan da suke, su tsunduma yawon duniya saboda tamkar an bata musu rayuwa ce.
Don haka yana da kyau iyaye su rika yin nazari kafin yunkurin bata auren ’ya’yansu. Sun rika yin nazari a kan abin da zai iya zuwa ya dawo. Su rika tuna irin illar da hakan zai iya janyowa ba ga ’ya’yan nasu kadai ba, har a cikin al’umma.
Idan uba ko uwa suka nace wajen raba auren ’ya babu gaira babu dalili, to wane mutum ne mai mutunci suke tunanin zai sake neman auren ’yar tasu idan ya samu labarin abin da ya faru?
Wani lokaci watakila yarinyar ce ta nace lallai sai ta auri mijin alhali ba shi da kudi, alhali suna neman wurin da za su huta ne. Ma’ana suna bukatar ’yarsu ta auri mai kudin da zai rika yi musu hidima. Wadansu iyayen kuma bayan sun aurar wa ’yarsu ga wani attajiri, idan karayar arziki ta same shi, sai su nemi raba auren.
Irin wadannan iyaye sun manta cewa komai nufin Allah ne. Sau nawa ne mace take auren mai kudi ya koma talaka? Kuma sau nawa aka samu wacce ta auri talaka amma aka wayi gari mijin nata ya zama hamshakin mai kudi?
Wadansu iyayen kuma kan yi kokarin hana ko raba auren ’ya’yansu ne saboda irin cutarwar da ake yi musu daga bangaren matar ko mijin.
Musamman a bangaren mata, a wasu lokuta sai ka tarar mijin da suka aura ya canja halin da aka san shi da shi tun da farko na kirki. Yakan yi biris da matar da ’ya’yan da suka haifa ta hanyar danne musu hakki. Ba abinci, ba sutura, ba ilimi ba sauran bukatu na yau da kullum. Kuma matar tana cikin tashin hankali tare da ’ya’yanta. To a irin wannan yanayi, babu laifi idan iyayen suka nemi raba auren bayan an bi duk matakan da suka dace amma abin ya faskara.
A wasu lokuta irin wadannan maza kan kaurace wa matan na tsawon lokaci. Ta yaya za ka kwatanta irin mazan da ke kaurace wa mata har na tsawon shekara da shekaru da sunan sun tafi neman kudi? Ko ba a fada ba, irin wadannan maza suna shiga hakkin matansu. Wadansu kan yi kurarin sun bar isasshen abinci a gida, wanda watakila za a dauki lokaci bai kare ba A sha’anin aure, ai ba abinci ne kawai hakkin da ya rataya a kan miji game da matarsa ba. Addinin Musulunci bai yarda don ka ba mace abinci kadai shi ke nan ka sauke hakkkin da ke kanka a kanta ba.
Na tabbata irin mazan da suke barin matansu suna tafiya wasu garuruwa kuma su shafe wata da watanni ba tare da sun koma ba, anya ba sa yin harka da wadansu matan a can?
Idan an samu masu jin tsoron Allah ne za ka tarar sun sake yin aure a can, amma ba su fada wa matansu na gida ba. Ke nan, sun tare a can wajen amarensu amma sun bar matansu na gida suna cikin halin kunci.
To duk iyayen da suka nemi raba irin wannan aure, ba za a ce sun yi kuskure ba.
Sai dai a wasu lokutan iyaye musamman mata kan yi kokarin raba auren ’ya’yansu ne ba tare da wani kwakkwaran dalili ba kamar yadda wadansu iyaye suka yi kokarin raba auren ’yarsu da take jin dadi a gidan aurenta kamar haka:
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta DuniyarHausa .com a wayarku ta hannu:
Download here

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

No comments:
Post a Comment