Author Fatima
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta DuniyarHausa .com a wayarku ta hannu:
Download here
Kungiyar kula da bola na Najeriya wacce aka fi sani da Public Private Participation, tace jihar Lagas ta zamo daya daga cikin birane mafi datti a duniya.
Mataimakin shugaban AWAM, Mista David Oriyomi, wanda ya bayyana hakan a ranar Talata, 18 ga watan Satumba a Lagas yayinda yake zantawa da manema labarai yace birnin ta zamo mafi datti ne sakamakon yunkurin da akeyi na hana ma’ikatan sharan yin aikinsu.
Oriyomi, ya bayyana cewa kaddamar da shirin Cleaner Lagos Initiative a 2016 da Gwamna Akinwumi Ambode yayi tare da kudirin ba kamfanin kasar waje mai suna “Visionscape” kula da ragamar aikin karban sharan ita kadai daga hannun 350 PSP, ne ya haddasa lamarin rashin bin ka’idan kula da sharan bolan.
A cewarsa hakan ya zoma AWAM a bazata domin babu wani tuntuba da akayi masu.
A baya munji cewa rahoton gidauniyar Bill and Melinda Gates na shekara, ta bayyana cewa Najeriya zata kasance da mutane mafi talauci a duniya a 2050.
A cewar shafin gidauniyar na yanar gizo, rahoton yayi duba ga nasarorin da aka samu a fadin duniya. A wannan shekarar, daga taron har rahoton zai mayar da hankali akan yawan matasa da zasu shafi cigaban duniya anan gaba.
Download here
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:


No comments:
Post a Comment