Author Fatima
Hafsan sojojin saman Najeriya Sadiq Abubakar ya bayyana cewa rundunar sa ta sayi akalla jiragen yaki talatin tun bayan hawan shugaba Muhammadu Buhari a karagar mulki kimanin shekaru uku da suka shude.
Hafsan sojin dai ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a yayin bude wasu muhimman ayyuka a makarantar koyon aikin sojan saman ta Najeriya dake a garin Kaduna.
Mista Sadiq Abubakar ya kuma kara da cewa rundunar ta samu sukunin gyara wasu jiragen goma sha takwas duk dai a karkashin shugabancin Muhammadu Buhari.
A wani labarin kuma, Jirgin kasan dake jigilar fasinjoji daga garin Abuja zuwa Kaduna a ranar Asabar yayi hadari kan hanyar sa daga garin Abuja zuwa Kaduna jim kadan bayan barin tashar sa dake a unguwar Idu, Kubuwa, birnin tarayya Abuja.
Majiyar mu dai ta tabbatar mana da cewa jirgin kasan dai haka zalika ya yi raga-raga da wata baiwar Allah inda ya markade ta ta yadda ba ma a gane ta kwata-kwata.

No comments:
Post a Comment