Sabbin labarai

Doko Android app dinmu ⬇ Download here

Duniya Abin Mamaki: wanda keson fara zuwa shakatawa a duniyar wata?

Author Maryam Ahmad

Yusaku Maezawa hamshakin mai kudi ne na kasar Japan da aka fara sani a matsayinsa na mai kada ganga a wata kungiyar mawaka.
Daga baya ya samu kudi a harkar sayar da kayan sakawa ta intanet, kuma an san shi a wajen Japan ta hanyar kashe miliyoyin daloli a wuraren baje-kolin zane-zane da ke cike da tarihi.
A halin yanzu dai burin Mista Maezawa ya dara zama kawai a duniyar 'yan Adam
Yana da burin zama fasinja farin fula na farko da zai fara tashi zuwa duniyar wata, a matsayin wani bangare na wani shiri tare da kamfanin Elon Musk, SpaceX.
Attajirin na Japan yana son ya yi tafiya da wasu masu yin zane-zane, a tafiyar da aka saka ran cewar za a yi a shekarar 2023.
Kawo yanzu dai Mista Maezawa, mai shekara 42, bai bayyana adadin kudin da ya biya domin tafiyar ba, lamarin da ya hada hamshakan masu kudi wadanda ba su damu da kasancewa a bainar jama'a ba.
Dan kasuwar na Japan ya fara sayar da tsaffin faya-fayen CD da wakoki a shekarar 1998 ta wani kamfanin da ya samar mai suna Start Today.
Harkar tasa ta ciniki ta hanyar wasika ta koma kan intanet a karshen karnin da ya gabata ya kuma kara kayayyakin sakawa cikin abubuwan da yaka sayarwa.
A farkon wannan shekarar, ya sanar da jaridar Japan Times cewar "Na kasance shugaban kamfanina a lokacin da nake yawo cikin kasar da kungiyar kade-kadena.
Da ya zama wani abin da ba zai yiwu ba in hada harkokin biyu, na zabi kamfanina - a wancan lokacin ina mai shekara 25 zuwa 26."
Ya kaddamar da kamfanin sayar da tufafin zamani ta intanet Zozotown a shekarar 2004, kuma ya zama biloniya a lokacin da yake da shekara 30 da 'yan kai.
A yanzu mujallar Forbes ta lissafa shi cikin a matsayin mutum na 18 da ya fi kudi a Japan inda yake da kudin da ya kai dala biliyan 2.9.
Kwanan nan ne kamfaninsa ya yi suna bayan ya kaddamar da kayan gwaji da mutane za su iya amfani da su wajen tura awon jikinsu da shafin kamfanin na intanet.
Ya kashe makudan kudade a manyan wuraren baje-kolin zane-zane, kuma ya kashe dala miliyan 110.5 kan wani babban zanen da Jean-Michel Basquiat na Amurka ya yi.
A lokacin ya ce ya yi shirin kaddamar da zanen ne a wani gidan tarihi a Chiba, inda nan ne garinsa.
A shekarar 2016, ya sake biyan dala miliyan 57.3 kan wani zanen Basquiat din na daban - mai suna Devil's Head.
A wata sanarwar da ya fitar ya ce ya ji zuciyarsa ta kada a lokacin da ya fara ganinsa.
A halin yanzu, hamshakin mai kudin yana shirin amfani da tafiyarsa Duniyar Wata domin ya bai wa masu zanen da zai tafi da su ilhama na manyan zane-zane.
"Za a tambaye su su yi wani abu bayan sun dawo duniya. Wadannan muhimman zane-zanen za su ba mu ilhamar kirkiro wasu abubuwa daga cikin kawunanm ," in ji mutumin mai son zuwa sararin samaniya.
Bayan Yusaku da Musk sun yi shelar tafiya duniyar watan ne dai aka kaddamar da wani shirin zane-zane mai suna #dearMoon.

Kawo yanzu dai ba a bayyana iya kudin da Mista Maezawa ya yarda zai biya na tikitinsa na zuwa duniyar wata ba, amma Mista Musk ya ce "kudi ne mai yawa".
Duk da haka, ana shakka kan ko Mista Maezawa da kuma masu zanensa za su iya zuwa su zagaye duniyar wata.
Tafiayar da suke son yi din za ta dogara ne kan wata roka da har yanzu ba a gina ta ba, kuma Mista Musk da kansa ya ce babu tabbacin cewa za a iya tayar da rokar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta DuniyarHausa .com  a wayarku ta hannu: 

Download here


Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:


No comments:

Post a Comment