A jawabin da ya fitar, ya bayyana cewa babu shakka akwai bukatar gwamnati ta gaggauta binciken musabbabin faruwar lamarin, wadda yaa wakana a bangarorin Abuja a ranakun Alhamis da Juma’a.
Ya ce akwai bukatar Najeriya ta fito da tsarin da zai magance sake faruwar wannan jijjigar kasa, ya-Allah ko dalilin hakar kasa ne ta faru ko kuma a’a.
“In dai akwai inda aka rarake karkashin kasa ana gina titin karkashin kasa ko yin wani gini a karkashin kasa, to wannan gini kan iya kumbura jijiyoyin kasa har su fara jijjiga.” Inji Matawal.
“Su kan su mazauna Abuja na matukar bukatar da a horas da su matakan gaggawar da ya kamata su dauka a cikin hanzari, idan irin haka ta sake kasancewa.
“Idan wannan jijjiga kaddara ce daga Allah Ta’ala, to fa sai a yi shirin fara kwashe mutane daga Abuja ana ficewa, domin ita babbar girgizar kasa fa ta kan fara ne da ‘yar jijjigar kasa, dalili, saboda karkatsewa da daddatsewar da igiyoyi ko jijiyoyin karkashin kasa ke yi ko kuma saiwa-saiwar da ke rike da farantin da ke tallabe da jijiyoyin karkashin kasar su kan su.” Gargadin Matawal kenan.
“Wato aman wutar duwatsu da girgizar kasa duk wani balbalin bala’i ne wadanda Najeriya ba ta ma taba tunanin yi musu shirin ko-ta-kwana ba. To saboda ba a taba shirya musu din nan ba, sai jikin mu ke ba mu cewa kamar ba mu ma san da su ba, ko kuma ba mu yarda za su iya faruwa a nan ba.”
Ya ce mataki mafi sauki da kuma saurin dauka idan irin haka ta faru, to a yi gaggawar ficewa daga inda ake, a kwashi yara da kananan dabbobin da za a iya runguma, a runtuma a guje zuwa cikin fili ko sararin da babu gine-gine kusa.

No comments:
Post a Comment