Author Maryam Ahmad
Download here
Shugaban kasa ya tafi tare da uwargidansa, Aisha Buhari.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, ya sanar da hakan ne cikin dare tare da hotunan saukarsu daga jirgi tare da uwargidansa inda jakadan Najeriya zuwa Amurka, Ambasada Sylvanus Nsofor; jakadan Najeriya zuwa majalisar dinkin duniya, Farfesa Tijjani Bande da ministar harkokiin wajen Najeriya, Geofrey Onyeama, suka tarbesa.
A ranan Asabar, fadar shugaban kasa ta sanar da cewa Buhari zai halarci taron majalisar dinkin duniya karo na hudu.
Yace: "Shugaba Muhammadu Buhari zai tafi New York gobe Lahadi domin halartan taron gangamin majalisar dinkin duniya UNGA37 wanda aka kaddamar ranan 18 ga watan Satumba, 2018."
Taken taron gangamin na wannan shekaran shine: "Ganin cewa majalisar dinkin duniya ta amfani mutane gaba daya'.
Babban abinda Buhari zai yi a Amurka shine jawabinsa da zai gabatar ga taron gangamin ranan Talata, 25 ga watan Satumba 2018 inda zai jaddada matakin da Najeiya take dauke wajen samar da zaman lafiya da tsaro."
Kana ana sa ran zai bukaci taimakon kasashen duniya wajen yaki da rashawa, dawo da kudaden sata da kuma yaki da ta'addanci."
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta DuniyarHausa .com a wayarku ta hannu: Download here
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:


No comments:
Post a Comment