Author Fatima
A wani hari da ‘yan bindiga suka kai wasu unguwanni da ke Karamar Hukumar Birnin-Gwari zuwa hanyar Kaduna, an yi garkuwa da mutane bakwai
A cikin mutanen da aka yi garkuwa da su akwai ma’aikacin gidan talabijin Najeriya NTA Yahaya Isah tare da matarsa da ‘ya’yansu biyu akan hanyarsu na dawo zuwa Kaduna bayan sun halarci wani sha’ani a Birnin-Gwari.
Rahotanni na bayyana cewa, a ranar Lahadin da ta gaba ta ‘yan bindigan sun yi garkuwa da mai unguwan Kirazo dake hanyar Birnin-Gwari zuwa Funtuwa, Mai Unguwan da aka fi sani da Basaw da kuma wani mazaunin kauyen Maigwari mai suna Dayyabu.
A yankin da ake garkuwan ne aka yi garkuwa da wani xan majalisar dokokin jihar Kaduna Salisu Haruna lokacin da yake hanyarsa ta zuwa Kaduna ranar Asabar.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar ‘yan sandan jihar Yakubu Sabo ya ce, hukumar ta samu rahoton garkuwa da Isah da wasu mutane biyu kuma su na iya bakin kokarinsu na ceto daga hannun masu garkuwan.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta DuniyarHausa .com a wayarku ta hannu:
Download here

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

No comments:
Post a Comment