Author Aisha Jega
Mata dayawa suna tafka wasu kusakurai da ya kamata ace sun gyara. Ko wacce mace ta kan so ta rinqa samun hutu a cikin gidan ta musamman idan mijin ta ko ita kanta tana da halin ďauko mai aiki. Amma yanzu abubuwa sun juya don masu aiki sun jefa wasu mata cikin tasku da tashin hankali. Haka nan samun wadannan labarai ya sanya wasu jin tsoron ďauko mai aiki ko da kuwa aikin gidan su zai kashe su. In kina da buqatar ďaukan mai aiki sai ki biyo ni don sanin abubuwa da dama akan 'yar aiki.
Wannan rubutun da yardan Allah zayyi bayani dallah-dallah kuma mata zasu fahimci abubuwa dayawa da suke yin sake dasu.
Farko dai WACECE MAI AIKI? Mai aiki dai zamu iya cewa baiwa ko bawan wannan zamani ne, banbancin shine wannan kamar hayansa kake yi wancan kuma siyan shi kake yi mallakin ka ne. Mai aiki 'yar adam ce kamar ki, hanyar da aka bi aka same ki ita ma shi iyayen ta suka bi suka same ta. Tana da uwa da uba da 'yan'uwa kuma suna son ta kamar yanda naki iyayen suke sonki. Mace ce ita kamar ki, kuma zata iya yin duk abun da kike yi a cikin gidan auren ki koda kina ganin bata waye ba. Saboda mutum ba dabba bane yana da hankali da tunani.
MASU AIKI SUN KASU KASHI BIYU
1. Mai aikin zuwa kullum: Wanda kun qayyade lokacin da zata zo aiki da lokacin tashin ta. Wata ma ba kullum bane kin bata ranakun zuwan ta. Irin wannan sai in tana unguwar ku a kusa da gidanki.
2. Mai aikin kwana: Itace wacce ake ďaukota zama dindindin, a kwana a tashi da ita, ta zama part of your family. Irin wadannan musamman daga wani gari ake ďauko su a kawo su aiki.
BINCIKEN MAI AIKI
Shin kin taba tunanin kafin ki ďauko 'yar aiki ki yi bincike a kanta? Da ita kanta mai ďauko masu aiki. To bari ki ji, in zaki ďauki mai aiki akwai abubuwan da ya kamata ki duba kafin ta shigo miki gida, gasu kamar haka:
1. Asalin mai aiki: A binciki asalinta, shin iyayen ta mutanen kirki ne. Sannan a binciki in da aure ko ba aure aka haifeta. A binciki tarbiyyan gidan su da irin abun da mutanen unguwa suke fadi game dasu. Domin rashin duba asalin ďan aiki ya 'bata aure da dama domin baki sani ba ko gidan mayu ne ko matsafa ba a ďauko masifa a kawo miki gida.
2. Tarbiyyan yarinyar a unguwar: Ba ko wane ďan qauye bane bagidaje kuma qauyukan da da yanzu akwai banbanci. Zaki ga yara qanana amma suna zina, sai a kawo ta kina ďauka bata san komai bayan ta girmeki a harkan don ita ba da namiji ďaya take yi ba. Tana zuwa gida kuma bata fita, gashi tana ci tana qoshi sai ta fara neman mijinki ko 'ya'yanki. Don haka In 'yar iskace ki canza wuri.
3. Addinin yarinyar: Ki tabbata an kawo miki wacce take zuwa islamiyya ko ba boko don ki samu sauqin wasu abubuwan. Idan jahila ce zaki sha wahalar zama da ita. Kuma zata iya cutar dake don ba tsoron Allah a ranta.
4. Ki san full address ďinta: Ko kuma ma ki je qauyen su in kina da lokaci. An sha samun masu aikin da suke tafka sata, wata har yara ta sata ta gudu dasu, saboda babu wanda yasan daga ina ta fito. Amma in ta san an san gidan su da qauyen su zata rinqa tsoron yin wasu abubuwan.
5. Lafiyar yarinyar: Kada a kawo miki mai aljanu su zo su shafi 'ya'yanki, ko mai wata cuta da zaku iya kamuwa dashi.
Idan wacce take unguwar ku ne yin binciken ta zai fi miki sauqi. Wainnan da ma wasu yana da kyau ace an kiyaye su. Kuskure ne ki ďauko wanda baki san komai game dashi ba ki a aje a gidanki.
Kada ku manta ana gadon mummunan hali da ďabi'a, kamar yanda ake gadon halin kirki da mutunci. Idan kika yi sake zaki sha mamakin mai 'yar aiki zata aikata miki wata rana. Na ga wani video a instagram da matar ta cewa yarinyar ta tafi ta gaji da ita, har zata fita sai ta ji hankalin ta bai kwanta ba da aka bude jakan kayan ta sai ta ga hotunan ta dana 'ya'yanta. Kuma da aka bincika tafiya zata yi a musu asiri, kin ga wannan ba abun wasa bane. Ta tafi amma ta sa ana turo miki da fitintinu a gidanki.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta DuniyarHausa .com a wayarku ta hannu:
Download here

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

No comments:
Post a Comment